MATA GA SIRRIN SOYAYYA DA BAZAWARI

MATA GA SIRRIN SOYAYYA DA BAZAWARI, 


Ita ma macen da take soyayyar aure da bazawarin da yake da mata daya ko fiye a gidansa, macece datafi sauran matan da muka ambata a baya aiki tukuri domin ganin ta samu shiga wajen manemin nata har kuma tayi sa'a amincewarsa ta zama matarsa ta aure.



Duk da yake wasu mata na ganin cewa auren mace mai mata yana da matsala da kuma wuyar gaske, ni kuma anawa ra'ayin da kuma nazarin ba haka abun yake ba, matsalar da mata suke fiskanta dai kwai shine, basusan sirrin soyayya da mazan da suke da mata a lokacin da suka zo neman auren suba. Shi yasa 'yan mata da damar gaske suke daukar cewa maza masu mata basu da dadin soyayya kokuma rashin sanin yaddazaki tafiyar da shi yasa ki rasa shi.
Sirrin duk wani namijin da yake da mace a gida ko yake da mata kuma ya fito yana meman kara wani auren shine, yana da dalilin daya sanya yake sha'awar kara wannan auren kuma yace ke yakeso ki zama matar tasa dai zai kara, to yana da kyau kiyi kokarin sanin dalilinsa na sha'awar karawannan aure domin yin nazari ko dalilin nasa ya isa ya zama hujjar da zaki iya aurarsa.



Da akawai wasu dalilan da sukan sanya ma suyi tunanin kara aure, da akwai na rashin son matan da suka aura tun a farko, da kuma dalilin kazanta ko rashin iya kwalliya, wani ya soma ne da auren bazawara yana neman ya kara da budurwa, wani kuwa da budurwa ya soma zai kara da bazawara, da akwai mazan da suke son hada mata masu bambamcin kabila ko al'ada kokuma launi na fata, da kuma mazan da dazaran mace ta soma tsufa suna sha'awar auro wata matar.
Da kuma wadanda rashin wadatan jima'i yake sanyasu su kara aure, wasu kuwa tarkon soyayya suke fadawa su kasa fitowa sai maganarc aure ya shigo, don haka duk wani na mijin da kikaga yana neman aure bayan yanada mata a gida koma mata fiye da daya, tabbas yana da hujja sai dai ba lalle bane hujjarsa ya zama hujjace mai gamsar da wanda yake fadawa ba.



Don haka babban kalubalen dake gaban kowace mace budurwace ko bazawara ta fahimci dalilin bazawari mai mata a gida da yazo nemanta da aure koda kuwa itace ta tsukanosa shi kuma ya fada kogin na sonta. Domin wannan shine sirrin maza a matakin farko da mace zata iya fahimtar namijin daya ke sonta dailinsa na son auren nata da kuma yadda yake tunanin zama da ita tare da matansa, muddin mace ta gano wannan tabbas idan har da gaske take tanason aurensa zata samu kansa cikin sauki.



Dazaran ki gamsu da dalinsa na sonki da aure bayan yana da mata a gida abu na gaba da yakamata ki sani game da sirrin maza magidanta masu neman kara aure shi ne yawan matansa da kuma yanayin zaman da suke yi, ma'ana suna gida daya ne dukkansu idan sun wuce daya ko kuma kowacce danata gidan ne kuma kina iya sani.Sai kuma kokarin sanin yadda yake zamansa da matarsa ko matansa a matsayinsa na mijinsu.


Wadannan sune manyan hanyoyin kuma matakan farko na soma fahintar mijin da zaki aure da kuma sirrin mazan da suke da mata a lokacin da mace take soyyay da su. Domin ta hanake zaki fahimci irin zaman lafiyar da zaki yi da shi a lokacin da kika shiga cikin kishiyoyinki idan gida guda zaki zauna da su. Haka kuma zaki fahimci inda matan suka kasa kekuma ki fisu tanan.


Sirrin maza masu mata da suka zo neman kara aure shine mace ta tabbatar da cewa a duk lokacin da irin wadannan mazan suka ziyarceta tayi kokarin faranta masa rai da kuma yi masa kisisinan da zai ji cewa matansa na gida tabbakar gumaka ne ya ajiye saboda rashin iya kwantar masa da hankali. Haka kuma ladabinki ki tabbatar da cewa ya wuce na yadda hankali zai kama, domin akasarin matan da suke cikin gidajen mazansu na aure basu cika damuwa da yi masu ladabi ganin sun kwanta dasu tsirara, don haka duk lokacin da namiji mai mata a gida yaga cewa matar da zai aura mai biyayyace nan take yake ji tamkar karya bar kofar gidansu ba daura masa aure da ita ba ko da kuwa ta gidan mai ladabi ce.


Shi ma namiji mai mata yana son ganin ya auri mace mai karanci buri ba mai yawan bani-bani ba, ganin yadda yake da nauyi a kansa don haka yana bukatar ganin cewa matar da zai aura mai saukin kai ce da kuma saukin yawan gabatar da bukatu ko da kuwa mai hannu da shuni ne manemin nata.

No comments:

Join our WhatsApp group

Join our WhatsApp group
Latsa nan domin shiga group din mu na whatsapp
Powered by Blogger.