MUHIMMAN ABUBUWAN DA ZAKI KULA DASU YAYIN DA KUKE SHIRIN AURE DA SAURAYINKI

SIRRIN DA NAMIJI: ABUBUWAN DA ZAKI KULA DASU YAYIN DA KUKE SHIRIN AURE DA SAURAYINKI



Bayan kin fahimci Saurayinki kunyi soyayya da Hira irin wacce Musulunci ya umurce ku kuyi, abu na gaba shine Ku fara Maganar Aure domin kuwa Babu amfanin soyayya Da Saurayi idan har ba Aure zakuyi ba. Kuma musulunci bai yarda da irin wannan Soyayya ba ko in ce Tarayya, tsakanin Da Namiji da Mace.


Abun da ya kamace ki kiyi a Yayin da suke soyayya da Saurayinki shine, Idan har aka kai matsayin da Soyayyar ku tayi nisa ki fara masa maganar Aure domin A fara shirye shiryen Auren Naku. Hakan zaisa idan ma ba da gaske yake ba ko kuma bai shirya ba zaki gan ya fara ja baya akan soyayyar ku. Idan kuma ya shirya sai ki tabbatar kun Tsara komai kamar yadda Addini ya tanadar.


Idan kuma ya amince aka fara maganar Auren naku, toh abinda ya kamace ki kiyi shine, kada ki kuskura ki saka Karya a cikin Hidimar bukin ku domin kuwa wannan shine babban kuskure da Ma’aurata sukeyi kamin Aure. Ki tabbatar da bakiyi kokarin yin abunda yafi karfi matsayin Gidanku ba, domin wannan na iya saka ki cikin damuwa a gidan Auren ki.

Kuma a duk lokacin da za’ayi aure yana da Mahimmanci musan cewa Addini ya riga ya tsara mana komai cikin Sauki, Sannan kuma akwai Al’adu daban daban wanda kuma idan har basu sabawa addini babu matsala za’a iyayi. Dan haka idan akwai wata al’ada da kike sha’awar yi amma babu halin yi a Gidanku, kuma Mijin baida halinyi toh KADA KI KUSKURA ki matsa masa akan sai anyi wannan al’adar domin kuwa Albarkacin Aure yafi yawa ga Auren da aka gina shi akan Tausayin Juna. Kuma Saurayin naki zai fi ganin Mutuncin ki da na gidan ku a yayin da yasan cewa Baki matsa mishi akan abunda yafi karfin sa.

Wannan Wani babban kuskure ne da Wasu Mata keyi tun kamin su shiga gidan Auren su, ganin anyi wani abu a bikin wance itama tanaso ayi a nata bukin.


Kada ki manta Tausayin Juna wani abu ne mai Mahimmanci a Zamantakewa, Sannan Gaskiya da Rikon Amana, ki tabbatar da Bakiyi wani abu ba domin burgewa ba sai dai dan Allah da kuma Irin soyayyar da ke tsakanin ki da shi Saurayin naki.
Allah sa mu gane gaskiya.

No comments:

Join our WhatsApp group

Join our WhatsApp group
Latsa nan domin shiga group din mu na whatsapp
Powered by Blogger.