WASU HIKIMOMIN GANE IDAN ANA SONKA DA GASKE, ALAMOMIN SO NA GASKIYA

HANYOYIN DA ZAKA GANE IDAN ANA SONKA DA GASKE, DOMIN GANE MASOYIN GASKIYA DA SOYAYYAR GASKIYA



Hikimomin Gane Idan Ana Sonka
Idan kana son ka gane da gaske ana sonka, wadannan sune alamomin. Wannan rubutu yana da dangantaka ne da duk wanda yake tantamar soyayyar da ake masa, ta haka ne zai gane, duk da cewa dai soyayya ta gaskiya ba a gane ta a lokaci kankani kasancewar tana shiga ne sannu a hankali. Ita soyayyar gaskiya tana toho ne da yaduwa a cikin zukatan mutane a yayin da ake zama ana fahimtar juna. Wani abin bakin cikin yanzu shine soyayyar gaskiya ba ta cika dorewa ba. Wani lokacin sai an yi nisa sai a ~ata ko ta lalace, Wannan bayani ya gudana ne ga duk wani masoyi da yake shakkun masoyiyarsa ko tana son sa ko ba ta son sa.

• Idan tana yawaita fada maka tana sonka kuma ka tabbatar da hakan, tana jin son sosai a zuciyarta, sannan kuma tana jin son ba tare da tana rokonka wani abu ba, sakamakon hakan ba ta jin bacin rai kuma ba ta bata maka rai.

• Idan tana magana ka rinka kula da idonta, wajen magana za ka iya gane mace in tana sonka idonta yana nuna alamun tausayi da soyayya ga wanda take so da kauna. Duk ta kwayar idonta za ka iya gane mace in mayaudariya ce ko dabara da wayo take maka. Shi ya sa aka ce abu mafi sauki da muhimmanci ka rinka kula da kwayar idonta wajen fahimtar son da take maka in dai tana matukar sonka za ka gani.

• Za ta rinka yin duk wani abu da ta san zai faranta maka rai. Mata suna nuna kulawa sosai ga wanda suka damu da shi, shine sai a yi maka abu ba tare da ka tambaya ba ko Ka nuna kana so ba, in dai an san ka damu da abin saboda son da ake maka. Za a yi don a faranta maka rai. Wannan duk alama ce ta ana sonka.

• In tana sonka babu ruwanta da wasu samarin, na san ba kowane zai yarda da haka ba. Amma soyayya ta gaskiya ido rufewa yake, in dai mace tana sonka idonta rufewa yake ba ta ganin kowa a gabanta sai kai. Kar ma ka damu kanka a kan da namiji saboda idan idon sun rufe babu kowa da ya mamaye zuciyar sai kai. To ka ga kenan tunaninta, jinta da ganinta duk naka ne.

• In tana matukar sonka za ta yi kokarin ta ga ta magance duk wata damuwa da ta shafe ka, da duk matsalar da ta dame ka za ta rinka jin duk wata damuwa taka kamar tata. Saboda haka idan dai har mace tana daukar damuwar wanda take tare da shi kamar yadda za ta dauki tata damuwar to a gaskiya wannan ita ma alama ce ta tana sonka kuma tana tare da kai.

• In tana sonka za ta rinka tinkaho da alfahari da samunka, da kuma nunaka a gurin ’yan’uwa da abokan arziki, kawaye da sauran su. Saboda in mace tana sonka gani take ka zama wani bangare na jikinta. Wannan ne zai sa ta rinka tinkaho da kai ba tare da jin nauyi ko kunya ba.

• In tana sonka za ta rinka fifitaka a kan ko wane abu, idan ma tana tare da wasu da suke tare da ita ka shigo kuma ta ji ta fi sonka to za ta fi fifitaka a kansu kuma za ka gane, saboda za ta fi son ta ga tana tare da kai ba tare da gajiyawa ba, da son yin waya da kai ba gajiyawa, sannan za ta rinka goya maka baya da nuna maka soyayya a kan za ta iya rabuwa da kowa saboda kai.

• Damuwa da kulawa da kai a duk lokacin da take tare da kai, mata suna son su rinka kula da wanda suke masa son gaskiya a cikin dadi ko rashin dadi, ko da lafiya ko babu lafiya kuma ba tare da nuna damuwa ko bacin rai ba. Wadannan alamomi sun isa su nuna maka mace tana sonka kuma tana tare da kai.


• Idan tana sonka za ta yawaita tambayar ’ya’uwanka da abokanka sannan za ta rinka girmamaka da duk wani abu da ka ke so, ba za ta so bata maka akan abin da ta san ka dauke shi da muhimmanci a rayuwarka ba. Misali ’yan’uwa da harkar kudi da harkar jin dadi, addininka da dai duk wani abu da ta san ya kunshi al’amurran rayuwarka. Irin abubuwan da ta san kana so, kamar in kana son barcin rana in matar ka ce ba za ta tasheka ba, don ita ma tana son duk wani abu da zai ba ka jin dadi. Saboda haka duk wannan yana cikin so da kauna.

No comments:

Join our WhatsApp group

Join our WhatsApp group
Latsa nan domin shiga group din mu na whatsapp
Powered by Blogger.