IDAN MACE TA KAMU DA SOYAYYA
Yadda ake gane mace ta kamu da soyayya,

Idan Mace Ta Kamu Da So
Saɓanin namiji, wanda ko ba ya magana sosai da zarar ya afka tarkon soyayya, to fa nan da nan bakinsa zai buɗe.
A tsammaninsa, shi ne ya fi cancanta ya yi magana, ya ja ra’ayinta ta hanyar dukkan maganganun da ya yi tsammanin za su iya faranta mata.
Amma yayin da mace ta fara soyayya, (a karo na farko). To ko da mai yawan magana ce, sai ka taras bakinta ya rufe. Sannan sabbin alamomin kunya za su iya bayyana a tare da ita. Wannan abu ne mai sauƙin ganewa a tare da mata. Idan har za ka yi nazarinsu, ko da kuwa a cikin gidanku ne.

No comments:

Join our WhatsApp group

Join our WhatsApp group
Latsa nan domin shiga group din mu na whatsapp
Powered by Blogger.