WATA SABUWA: RAHAMA SADAU TA SAKE JAWO KACE-NACE AKAN WANI HOTO DA TAYI TANA SUMBATAR MACE YAR UWARTA

Jaruma Rahama Sadau ta sake shiga sabon cece-kuce akan sumbatar wata mace 'yar uwarta Sai dai wasu mutane na ganin cewa da gangan 'yan fim suke yin abubuwa na jan magana domin kada a manta da su Jarumar ta wallafa hoton ne a shafinta na Instagram inda sanya hoton keda wuya mutane suka yo caa kanta Jaruma Rahama 


Jaruma Rahama Sadau tayi kaurin suna a masana'antar Kannywood wajen sanya maudu'in da za ayi ta kace-nace a kai, zamu iya cewa tun farkon bayyanar ta ya zuwa yanzu jarumar ba ta shafe watanni uku ba tare da tayi wani abu da zai jawo magana a kafafen sadarwa ba. 

Koda yake wasu na ganin da gangan 'yan fim da mashahuran mutane kanyi abubuwa na jan magana don kar a mance da su, domin wasu sunyi ittifaki da zarar an daina jin duriyar ka tofa kasuwar ka ta mutu kenan don haka sun gwammace ayi ta batun su koda na Allah wadai ne dan dai sunansu da fuskokinsu su cigaba da karakaina a kafafen sadarwa da mujallu. 

KARANTA: BATA SUNA: KOTU TA BADA UMARNIN CIGABA DA TSARE TSOHUWAR JARUMAR FIN SADIYA HARUNA A GIDAN GYARA HALI

A yau wannan jaruma dai wani hoto ta wallafa a shafin ta inda aka ganta tana sumbatar wata mace 'yar uwarta inda wallafa hotunan keda wuya akayi caa a kanta da korafi inda har wasu shafuka suka fara wallafa hoton suna fashin baki a kai. 


Koda yake mu baza mu kalli wannan ta fuskar da akasarin mutane ke kallon abun ba in muka yi la'akari da cewa a 'yan kwanakin nan mafi yawancin hotunan jarumar da mata 'yan uwanta tana kusantar su sosai fiye da kima wanda zamu iya danganta hakan da karatu da tayi a kasar waje wanda hakan ba komai bane a gurin turawa masu jajayen kunnuwa, amma a nan gida hakan ya zama abin magana. 

No comments:

Join our WhatsApp group

Join our WhatsApp group
Latsa nan domin shiga group din mu na whatsapp
Powered by Blogger.