BATA SUNA: KOTU TA BADA UMARNIN CIGABA DA TSARE TSOHUWAR JARUMAR FIN SADIYA HARUNA A GIDAN GYARA HALI

Wata kotun majistare mai zama a Kano ta bada umarnin cigaba da tsare sananniyar tsohuwar jarumar Kannywood, Sadiya Haruna Idan bamu manta ba furodusa Isa A. Isa ne ya maka ta gaban kotu sakamakon zarginta da yake da bata masa suna  Jarumar ta fito kafafen sada zumunta ta sanar cewa sunyi auren mutu'a da furodusan tare da kiransa dan luwadi


Wata kotun majistare mai zama a Kano ta bada umarnin tsare sananniyar tsohuwar jarumar Kannywood din nan, Sadiya Haruna akan zarginta da ake da bata sunan furodusa Isa A. Isa. An gurfanar da wacce ake zargin ne akan laifin bacin suna wanda yaci karo da sashi ma 391 na Penal Code kamar yadda Daily Trust ta ruwaito. Amma ta musanta laifinta tare da zargin laifin da aka karanto mata. Lauyan wacce ake zargi, Y. A Sharif ya bukaci kotun da ta bada belinta amma dan sandan mai gabatar da kara, Jacob Yaduma, ya soki bukatar belin.

KARANTA: WANI MUTUM MAI YARA 100 YA KARA AUREN MATA HUDU DOMIN BUKATAR KARIN HAIHUWA DA YAKE

Yaduma ya ce wacce ake zargin zata iya tsallake belin ko kuma lalata binciken da 'yan sanda ke yi bayan belin. Mai shari'a, Jastis Muntari Dandago, ya dage bada hukunci akan belin zuwa ranar Juma'a, 18 ga watan Oktoba, 2019. Alkalin ya bada umarnin cigaba da tsare jarumar a gidan gyaran hali har zuwa lokacin da za a dubi bukatar belin nata. 

No comments:

Join our WhatsApp group

Join our WhatsApp group
Latsa nan domin shiga group din mu na whatsapp
Powered by Blogger.