WATA MATA TA SAYARDA TAGWAYEN JARIRANTA MILIYAN3 DOMIN BIYAN BASHI DA SAYEN SABUWAR WAYA SALULA

Bayan biciken da ’yan sanda suka gudanar sun kama wata uwa a kasar China, wadda ta sayar da tagwayen jariranta kan Dalar Amurka 9,100 (kimanin Naira miliyan 3 da dubu 285 da 100) don ta biya bashin da ake bin ta sannan ta sayi sabuwar wayar salula samfurin smart phone.


A cewar jaridar China Ningbo Ebening News , matar wadda ake kira da
sunan mahaifinta wato Ma, tana da shekara 20 ta sayar da tagwayen
jariran ne, saboda tsananin bashi da takura da take ciki. Mahaifiyar
jariran ta ce, ta sayar da jariran ne saboda ta same su ne ba ta hanyar
aure ba, ba ta son yaran su girma ba tare da suna ganin mahaifinsu
ba, inda ta bayyana cewa mahaifin jariran mai suna Wu, ya fada mata
cewa bai bukatar ’ya’yan da ta haifa.

KA KARANTA KUMA: MAHAIFIYATA TA TSINE MIN ALBARAKA SABODA NA KOMA ADDININ MUSULUNCI

Abin mamaki ne yadda Ma, ta yi kokarin samun masu sayen jariran da
ta haifa wata daya kacal. Amma kafar labarai ta ZaoBao ta bayyana
cewa, ’yan sandan sun bankado haka ne lokacin da suke wani bincike
mai alaka da irin wannan sai suka gano yadda ake gudanar da cinikin
jariran, bayan sun tsaurara bincike sai ’yan sandan suka gano an riga
an sayar da jariran ga wadansu ma’aurata biyu a Lardin Anhui, masu
suna Fuyang da Suzhou a kan Naira miliyan 3 da dubu 285 da 100.


Rahotan ya kara da cewa, mahaifin jariran baya nan lokacin da uwar
jariran ta haihu, sai da hukuma ta kama Ma, sannan mahaifin ya
gabatar da kansa. Ma, ta bayyana wa ’yan sanda cewa, bayan ta sayar
da jariran ta raba kudin don biyan bashin banki da mahaifin jariran ya
ci, yayin da sauran kudin ta yi amfani da su wajen sayen sabuwar
wayar salula. Wu, ya kasance yana ci gaba da biyan bashin kudaden
cacar da yake yi.

Jami’an ’yan sandan sun yin kokarin karbo jariran daga Anhui tare da
mika su ga iyayen Ma. A yanzu haka an tsare iyayen jariran don yanke
musu hukunci inda suke jiran shiga gidan yari na wani lokaci. Bayan
tsare mahaifiyar jariran da mahaifin tagwayen duk sun kashe kudaden
da suka sayar da jariran.

No comments:

Join our WhatsApp group

Join our WhatsApp group
Latsa nan domin shiga group din mu na whatsapp
Powered by Blogger.