BAKIN WATA MATA YA TSAYA A BUDE YAKI RUFUWA A LOKACIN DA TAYI DARIYA

Likita ya yi kokarin rufe bakin wata ’yar kasar China bayan ta yi dariya,inda muka-mukinta ya ki komawa daidai.


Wannan lamari ya faru ne a ranar 1 ga Satumban nan lokacin da matar
take cikin wani jirgin kasa a hanyarta ta zuwa tashar jirgin da ke
Kudancin Guangzhou. Dokta Luo Wensheng, na cikin fasinjojin jirgin
wanda ya taso daga garin Kunming babban birnin Yunnan da ke Kudu
maso Yamma, kuma an yi wa matar aikin a asibitin Liwan wata cibiya
ta Asibitin Koyarwa na Jami’ar Guangzhou bayan likitan ya samu
sanarwar gaggawa ta kafar labarai don bayar da agajin gaggawa ga
fasinjar.


Da jin sanarwar neman agajin sai likitan ya yi gaggawa zuwa don
taimaka wa fasinjar da bakinta ke bude ya ki rufuwa, inda hakan ke
nuna cewa tana fuskanta matsalar shanyewar wani bangaren muka-
mukinta. Sai dai an gano ba ta da cutar hawan jini. Wani da yake
magana da matar ce ya fahimci cewa, bakinta ya ki komawa yadda
yake bayan ta yi dariya mai karfi.


“Matar ta yi ta zubar da yawu dalalal bayan bakinta ya ki rufuwa,
kuma da farko na yi tunanin tana dauke da cutar shanyewar barayin jiki
ne,” Luo Wensheng, ya bayyana wa kafar labarai ta Guancha News.
“Ganin halin da take ciki sai na yi mata gwajin hawan jini tare da yi
mata wasu tambayoyi, sannan na fahimci cewa, lallai ta gaza amfani
da muka-mukinta,” inji shi.

KARANTA KUMA: KASH! FUSHI YA SA WANI MUTUM YA KASHE MAHAIFIYAR MATARSA DA KANWARTA DA DANTA JARIRI

Duk da yake Luo, ba kwararre ba ne a fannin kiwon lafiya, sai ya
kasance abin ya yi masa wani iri ta yadda ya rasa hanyar da zai bi don
saita fuskar matar. Sai ya fada mata cewa zai taimaka mata amma
abu ne mai hadarin gaske a saita muka-mukin. Amma duk da haka
matar ta bukaci ya gwada koda zai iya.


Luo, ya kara da cewa, “Wannan matar duk jijiyoyin jikinta sun yi rauni
kamar ba ta da lafiya. Kamar yadda likitan farko da ya duba ta ya
sanar. Na bai wa matar shawara a kan ta tafi asibiti, amma sai
ma’aikatan asibitin suka ce akwai sauran awa daya kafin su isa inda
za su tsaya. Sai na fahimci cewa, matar na cikin damuwa a wannan
lokaci, ganin haka sai na ci gaba da kokarin saita muka-mukinta ta
yadda bakin zai rufu.”


A wannan lokacin da Dokta Luo, ya yi kokarin saita muka-mukinta a
karshe matar ta ji zafi matuka, amma kuma ya yi nasara. Hakan ya sa
ta rufe bakin. Matar ta yi wa Luo godiya mai yawa, ta ce, muka-
mukinta ya fara gocewa ne lokacin da take dauke da juna biyu saboda
tana yawan amai. A cewarta idan muka-mukin mutum ya taba gocewa,
akwai yiwuwar ya sake yin haka, musamman lokacin da yake yin
hamma ko dariya kuma ya bude bakinsa sosai.

No comments:

Join our WhatsApp group

Join our WhatsApp group
Latsa nan domin shiga group din mu na whatsapp
Powered by Blogger.