WANI MUTUM MAI YARA 100 YA KARA AUREN MATA HUDU DOMIN BUKATAR KARIN HAIHUWA DA YAKE

Wani mutum dan kasar Uganda mai yara 100 ya karo mata
hudu sakamakon Karin bukatar haihuwa da yake.
Nulu Ssemakula mai shekaru 94 a duniya mazaunin kauyen
Ruyonza ya kara fadada iyalansa.

Ssemakula musulmi ne wanda ya sake farali a shekara 1977
kamar yadda jaridar Ugandan Monitor ta ruwaito.
Ssemakula wanda ya yi nasarar fadad iyalinsa na da mata
sama da 19 wadanda suka Haifa masa yara 100 kuma a
halin yanzu yana bukatar kari. Karamin dansa yana da
watannni 10 a duniya kuma amaryarasa mai shekaru 24 na
da cikin wani dan.

A halin yanzu yana tare da ‘ya’yansa 66 kanana. A yayin da
awasu daga cikin yaransa suka haifa masa jikoki, kakan y
ace shi kuwa yana bukatar Karin haihuwa, a don haka ne ya
karo mata 4.

Ssemakula ya auri matarsa ta farko ne a shekarar 1952
wacce bata dade bay a karo mata abokan zama 5.

“Matana 4 suka rasu a gidana, wasu kuma da suka nuna
bazasu iya zama dani ba sun tafi sun barani da yara. Zan
kuma kara auro wasu matan in har ina da sauran kwana. A
wajen mata da yarana nake samun nishadi. Su ne gaskiyar
arzikina.” in ji Ssemakula.

A halin yanzu, Ssemakula ya gina masallaci da makarantar
firamare da kuma in jin tatsar nonon shanu don kula da
iyalinsa.

No comments:

Join our WhatsApp group

Join our WhatsApp group
Latsa nan domin shiga group din mu na whatsapp
Powered by Blogger.