AN GARKAME GIDAN HORAS DA KANGARARRUN YARA DAKE GARIN DAURA BAYAN ZARGIN LUWADI DA CIN ZARAFIN BIL ADAMA A GIDAN

Rundunar Yansandan jahar Katsina ta bada umarnin garkame gidan horas da kangararrun yara dake mahafar shugaban kasa Muhammadu Buhari, watau garin Daura, inji rahoton kamfanin dillancin labarum Najeriya, NAN.

Wannan gida da ake kira da suna gidan Malam Bello ya shahara matuka wajen horar da kangararrun yara a garin Daura, jahar Katsina da ma sauran yankunan Arewacin Najeriya.

A ranar Litinin, 14 ga watan Oktoba ne kwamishinan Yansandan jahar Katsina, Sanusi Buba ya bada umarnin rufe gidan yayin daya kai ziyarar gani da ido tare da yan jarida da sauran masu ruwa da tsaki, inda yace ana cin zarafin bil adama a wannan cibiya.


Akalla yara 360 ne suka tsere daga wannan gida bayan sun balla dakunan da ake tsare dasu a ciki, haka zalika kwamishinan yace halin da yaran suke ciki a wannan gida abin dubawa ne, don haka yace zasu karade kananan hukumomin jahar guda 34 don bankado ire iren cibiyoyin nan.

Kwamishina Buba ya nemi duk iyayen da suka san akwai yaransu a wannan gida dasu zo dauke da wata kwakkwarar shaida domin amsan yaransu da kansu, a cewarsa “Babu wata doka da data halasta cin zarafin dan adam haka.”

Shi ma a nasa jawabin, mai martaba Sarkin Daura, Alhaji Faruk Umar Faruk ya yi kira ga rundunar Yansanda da ta gudanar da cikakken bincike a kan lamarin, sai dai ya nemi Yansandan da su yi adalci a yayin binciken nasu

No comments:

Join our WhatsApp group

Join our WhatsApp group
Latsa nan domin shiga group din mu na whatsapp
Powered by Blogger.