TSOHUWA MAI SHEKARA 56 TA YANKE MAZAKUNTAR MIJINTA MAI SHEKARA 61

TSOHUWA MAI SHEKARA 56 TA YANKE MAZAKUNTAR MIJINTA MAI SHEKARA 61


Wata mata mai suna Victoria Frabutt yar shekara
56, ta yanke al'auran mijinta Mr. Frabutt dan
shekara 61 bayan ta daure shi daram a yanayi na
killacewa, daga bisani ta yanke mazakutansa da
wuka.


Shugaban yansanda masu bincike Chief Detective
Jason Wank, ya ce , "Mun sami kira ne da karfe 4
na asuba a wani gida da ke Newport, Carolina na
arewa (Kasar Amurka), sai muka tarar da matar
Frabutt ta killace shi kuma ta daure shi, daga bisani
ta yanke mazakutansa.


 Mun dauki guntun
mazakutan muka dora a kan kankara sai muka
garzaya da shi asibiti bisa tunanin ko likitoci za su
yi kokarin hada mazakutan".


Yansandan sun kama Victoria kuma suna gudanar
da bincike, daga bisani majiyar yansanda ta ce za
su gurfanar da ita gaban Kotu.


har zuwa yanzu dai babu wani bayani kan dalilin da ya sa Victoria ta
aikata wannan aiki.

No comments:

Join our WhatsApp group

Join our WhatsApp group
Latsa nan domin shiga group din mu na whatsapp
Powered by Blogger.