KOTUN ZABE TAYI WATSI DA KARAR ATIKU NA PDP SHUGABAN KASA MUHAMMADU BUHARI YAYI NASARA

KOTUN ZABE TAYI WATSI DA KARAR ATIKU NA PDP SHUGABAN KASA MUHAMMADU BUHARI YAYI NASARA 

Bayan kwashe akalla sa'o'i takwas ana zaman kotu
kan shari'ar dake tsakanin shugaba Muhammadu
Buhari na APC da Atiku Abubakar na PDP,
shugaban kwamitin Alkalan kotun, Mohammed
Garba, ya yi watsi da karar da PDP da Atiku suka
shigar. Kotun zabe ta yanke hukuncin cewa shugaba
Muhammadu Buhari ya cancanci yin takaran
kujeran shugaban kasa saboda yana da kwalin
karatun da ake bukata har fiye da haka.


Kotun zaben shugaban kasa ta yi watsi da zargin
cewa dan takaran kujeran shugaban kasa karkashin
jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Atiku
Abubakar, ba haifaffan dan Najeriya bane kuma bai
cancanci takaran zabe. Kotun ta yi watsi da ikirarin
jam'iyyar PDP da Atiku cewa shugaba Muhammadu
Buhari ya yi amfani da yan sanda da sauran jami'an
tsaro wajen magudin zabe. Kotun ta ce akwai tafka
da warwara saboda ta yaya PDP da Atiku za suce
jami'an tsaro sun yi magudi kuma su manta da su
lokacin shigar da kara kotu.


Alkalin kotun ya soke dukkan bukatar da hukumar
gudanar da zabe ta kasa mai zaman kanta INEC ta
gabatar na watsi da karar jam'iyyar PDP da Atiku
Abubakar. Hukumar INEC ta bukaci kotun zaben ta
yi watsi da karar PDP saboda daya daga cikin
lauyoyinta, Dakta Livy, ba sahihin lauya bane.
Hakazalika INEC ta bukaci kotu ta soke bukatar
PDP da Atiku na cewa shugaba Buhari bai cancanci
yin takara a zabe ba. Misalin karfe 30, Alkalan
kotun zaben shugaban kasa karkashin jagorancin
Alkali Garba Muhammad, sun zauna kuma komai
ya kankama.


Shugaban jam'iyyar APC, Adams Oshiomole;
ministan ayyuka da gidaje, Babatunde Raji Fashola,
Shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa, Abba
Kyari, ministan kwadago, Cris Ngige; tsohon
gwamnan jihar Bauchi, Mohammed Abubakar, sun
isa kotun. Shugaban jam'iyyar PDP, Uche Secondus,
lauyoyin jam'iyyar PDP, Dakta Livy, Mike Ozekome,
sun isa kotu.


Daga cikin wadanda ke kotun akwai, gwamnan jihar
Plateau, Simon Lalong; gwamnan jihar Kebbi, Atiku
Bagudu; tsohon shugaban EFCC, Nuhu Ribadu.
Kawo yanzu, lauyoyi biyu sun isa kotun; Cif Charles
Edosomwan na jam'iyyar APC, da kuma Sam
Ologunoria na hukumar INEC. Rana ba ta karya, sai
dai uwar da taji kunya - Allah ya kawo mu ranar 178
bayan kammala zaben shugaban kasa a ranar 23 ga
Febrairu, 2019 inda hukumar gudanar da zabe ta
kasa mai zaman ta INEC ta alanta shugaba
Muhammadu Buhari matsayin wanda ya lashe
zaben.


Bayan sanar da sakamakon zaben, jam'iyyar PDP
da HDP sun shigar da kara kotun zaben shugaban
kasa domin kalubalantar wannan sakamako. Daga
baya, jam'iyyar HDP da dan takararta suka janye
kararsu daga kotun bisa wasu dalilai, amma PDP ta
ce sam sai ta ga abinda ya kwancewa kura zani.

No comments:

Join our WhatsApp group

Join our WhatsApp group
Latsa nan domin shiga group din mu na whatsapp
Powered by Blogger.