TSOHON MIJINA YAYI MUN ASIRI TUNDA YA SAKE NI BA WANDA YA SAKE CEWA YANA SONA. (BAZAWARA)

Wani miji, mai suna Akintayo Kalejaye, da matarsa, Funmilayo Kalejaye,
sun bayyana a gaban wata kotun gargajiya da ke Mapo a
garin Ibadan, jihar oyo, domin neman kotun ta basu takardun
shaidar cewa aurensu ya mutu shekaru biyu da suka gabata.


Miji da matar na yi wa juna zarge-zarge masu nauyi da suka
hada da cin amanar aure, rashin ganin girma juna, da kuma
nuna wa jutansu keta da mugunta a bayyane.



Da take bayyana dalilanta na amincewa ta gurfana a gaban
kotun domin neman shaidar mutuwar aurensu, Funmilayo ta
shaida wa alkalin kotu cewa, "miji na ya wulakantar da ni da
'ya'yan mu biyu da muka haifa tare, bai damu ba ko mu mutu
ko mu rayu .



"Ba ya iya sauke nayin mu da ya rataya a wuyansa, amma a
hakan ya je ya kara aure a wani wurin ba tare da sani na ba, a
yayin da gidan da muke ciki ma ni ce ke biyan kudin haya.


"Akintayo shaidanin mutum ne mai mugun hali, saboda kafin na
bar gidansa sai da ya je wurin wani boka a Ijebu Ode yasa aka
yi min asirin da maza za su daina sha'awa ta.



“Tun da na bar gidansa har yanzu babu wani namiji da ya taba
cewa yana so na. Ina rokon wannan kotu ta tilasta wa Akintayo
yasa a warware asirin da aka yi min ko na samu canji a
rayuwata," a cewar Funmilayo.



Kazalika, Funmilayo ta zargi mijinta nata da neman mata
barkatai, lamarin da yasa tuntuni alaka a tsakaninsu ta lalace.

No comments:

Join our WhatsApp group

Join our WhatsApp group
Latsa nan domin shiga group din mu na whatsapp
Powered by Blogger.