WANI MATASHI YAYI WA BUDURWA YAR SHEKARA 14 FYADE BAYAN YA ZUBA MATA WIWI A CIKIN ABINCI

Wani matashi mai suna Innocent Ifunayachi mai shekaru 34
ya yaudari budurwa ‘yar shekaru 14 inda ya sanya ma ta garin
tabar wiwi a indomi, bata fargaba taci ta fita hayyacin ta anan
ya yi mata fyade.


Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan Lagos DSP Bala
Elkana, ya shaida wa Aminiya cewa a ranar Larabar da ta
gabata ne dangin yarinyar suka shigar da kara a ofishin
rundunar ‘yan sandan da ke Bariga a Legas lamarin da ya kai
ga kame matashi.


Ya ce, matashin yakan ziyarci dangin yarinyar, kana a lokacin
da zai yi aika-aikar ya ziyarci gidan kamar yadda ya saba ko da
yaje ya iske yarinyar ta tasa abinci a gaba zata ci sai da ta
tashi domin ta debo masa ruwa ya sha kafin ta dawo ya
barbada mata garin tabar wiwi ko da taci abincin ta fita
hayyacin ta sai ya yi lalata da ita.


DSP Bala Elkana, ya ce wanda ake zargin ya amsa laifinsa za
kuma a gurfanar da shi a gaban kotu yayin da aka kai yarinyar
asibiti domin bincikar lafiyar ta.


Haka zalika Bala Elkana, ya shaida wa Aminiya cewa, a ranar
Larabar ofishin ‘yan sandan da ke Bariga ya samu koken wasu
iyali da suka ce wasu gugun matasa sun yi wa ‘yar su mai
shekaru 13 fyade kuma har ta dau ciki.

DAYA DAGA CIKIN WANDA AKE ZARGI

Ya ce, wadanda ake zargin sun hadar da Kazeem Bello mai
shekaru 26 da Dayo A Maker dan shekaru 24 dukan su na
zaune ne a Unguwar Elaje a yankin Bariga, wadanda ake zargi
da sun hadu suka yi wa yarinyar ‘yar shekara 13 fyade kuma a
sanadin haka ne ta haifi ‘ya mace makwanni 5 da suka gabata,
ya ce wanda ake zargin sun yi barazanar kashe yayrinyar idan
ta bayyana abin da ya faru, sai dai ta sami kwarin gwiwar
fadawa iyayen ta ne bayan da waxanda ake zargin suka yi
yunkurin yi wa kanwarta fyade.


DSP Bala Elkana, ya ce an kama daya daga cikin wadanda ake
zargin mai suna Dayo yayin da dayan ya ranta a na kare inda
rundunar ta bayar da sanarwar lalubo shi.

No comments:

Join our WhatsApp group

Join our WhatsApp group
Latsa nan domin shiga group din mu na whatsapp
Powered by Blogger.