ALAMOMI 10 DA ZAKI GANE NAMIJI YA KAMU DA SONKI KO BAI FURTA MIKI BA





Sau da yawa mata sukan rasa namiji sonsu ne ko kuma shakuwa ce, ko abota musamman ma idan bai furta ba. Ga kadan  daga cikin wadan su alamomin da za su tabbatar maki lallai
Namiji na son ki, so kuma na gaskiya da soyayya.
1. KULAWA
Idan namiji yana matukar sonki, za ki rika samun kiran wayar
sa akoda yaushe, baya iya zama na tsawon lokaci ba tare da
ya kira yaji lafiyar ki ba. YakanYakan
so ki zama farkon wacce zai yi Magana da ita bayan tashin sa
daga bacci, haka kuma ta karshe da zai yi sallama da ita kafin
ya kwanta. Zaki rika samun sakon sa na wayar sadarwa(SMS).
Haka kuma idan kika masa flashing duk abinda yake yi zai
ajiye sa, ya kira wayar ki, ko ya dawo maki da sakon da kika
tura masa. Yar uwata ki kula namijin da baya damu da ya kira
ki ba, sai in ke kin gaji dan kanki kin kira sa, ko kin tura masa
sako, toh baki cancanci bata lokacin ki garesa ba.


2. TAUSAYI
Wani feeling ne da ke ratsa zuciyar duk wani namiji da ya
kamu da ciwon son mace. Tausayi yana daya daga matakan
farko da ke tabbatar wa mace lallai namiji yana gab da, ko
kuma ya kamu da sonki. Zaki ga abu kadan wanda bai taka
kara ya karya ba, namiji yana tausayawa mace, ciwo kadan
zaki ga yana nuna matukar kulawar sa da tausayin sa gare ki.
Yar uwa ki kula duk namijin dayaya jin tausayin ki, toh da wuya
yana maki son gaskiya.


3. KASANCEWA DA KE
Namiji kan so kasancewa tare da wacce yake so akoda
yaushe, baya gajiya da ganinta, duk yanda ba yada lokaci zai
saman maku lokaci don kasancewa tare da ita. Duk namijin
da baya kiran ki, sai dai ke dan kanki ki nemi ko hado, toh
shima yar uwa ina maki tsoron in wannan namijin da gaske
yana sonki. Saboda wanda ke sonki na gaskiya, yana son
kasancewa da ke



4. SATAR KALLUN KI
Namijn da ya kamu da sonki, baya gajiya da kallun ki. Idan
kuna tare ki kula, abu kadan zaki yi, zai tsora maki ido, wani
lokaci ma zaki kama sa yana satar kallun ki. Haka kuma zai
rika kokari ya tausasa idon sa wurin Magana da ke, in kika
kula zaki iya hango tausayi da soyayya a idon sa.



5. GABATAR DA KE GA FAMILY SA
Duk Namijin da ke kaunar ki saboda Allah, zaiyi kokarin
gabatar da ke ga yan uwansa da abokanin sa. Baya jin kunya
ko wani haufin nuna ki a matsayin wacce yake so, yake kuma
fatan zama uwar 'yayan sa. Yar uwata ki kula, duk namijin da
kike zaune da shi, yana maki boyon kisan asalin sa, ko iyayen
sa, da abokanin sa, toh wannan namiji yana da wata manufa
daban gareki, yar uwa kiyi hakuri ki kama gaban ki, ina shaida
maki zai bata maki lokaci ne ga banza.


6. YARDA DA AMINCI
Namiji na yarda da amincewa ga macen da yake so. Zai rika
gaya maki sirin sa, musamman dangane ga abinda ya shafi
aikin sa. Zai gaya maki sirri kansa da yake tsoron gayawa
abokanin sa, saboda ya yarda da ke, baya taba tunanin zaki
tuni asirin sa. Idan namiji na maki boye boyen sirrukan sa, toh
ki bincike son da yaje maki.


7. KYAUTA
Kyauta na daya daga cikin alamomin da za su tabbatar maki
cewa Namiji na sonki, so na gaskiya. Wanda ke sonka baya jin
kiwar ma kyauta, ko da ko mutunen nan talaka ne, akoyaushe
fatan sa yayi abinda zai faranta maki rai, ta hanyar saya maki
wani abu ko mai kankantar sa, muddin yasan zai sayya ki farin
ciki. Sai dai ba lallai bane asamu ko wane namijin a hakan,
saboda shish alkhairi daga jini ne, wani duk son da yake maki,
sai ki same sa marowaci, baya iya wa ko kansa alkhairi balla
ya yi maki. Yar uwa sai ki kula in dai kin samu wasu daga cikin
alamomin da a ka kawo, amma kuma kin same sa da halin
rashin maki kyauta, sai kiyi hakuri, rowar ajinin sa take.


8. ABOKANAI
Abokanai suna daga cikin alamomin da zaki fahimce cewa
namiji yana kaunar ki. Ki kula in abokanin sa na gayama ki
cewa baya da aiki sai masu hirar ki, abo kadan zai ce "wance
kaza" toh wannan mutum yana sonki.


9. TSARA RAYUWAR SA DA KE
Yar uwa ki lura, a duk lokacin da kuna tare da shi, yana kawo
zancen auren ku, kamar ya ce maki; lokacin auren mu za ayi
kaza, ko kuma yayan mu kaza, ya na dai kokari tsara rayuwar
sa tare da ke.
Toh wannan mutunen yana maki so na gaskiya, so kuma na
Aure.


10. SHAN MINTI
A duk lokacin da Namiji yake nuna zalamar sa gareki, kamar
son yayi maki kiss, ko ya rungume ki, toh wannan ba saurayin
kwarai ba ne. Duk namijin da ke sonka sabida Allah, yake
kuma muradin ki zama uwar 'yayan sa, ba zai fito maki da
kwadayin sa a fili ba, har yana kokarin ya sa ki sabawa
ubangijin ki. Yar uwa ki kula da irin dangin wayan nan samarin
na zamani, saboda su suka yi yawa awannan lokacin. Kina
kuskuren da kika bari ya fara taba ki da sunan wai ya nuna
maki yanda yake jinki a ransa, ta hanyar rungumar ki, ko yi
maki kiss, toh tabbas shaidan zai shiga, har ya kai ku da ku
afkawa juna, daga nan duk son da yake maki zai guje ki,
muddin ya samu abinda ya ke so. In kuma ma Allah ya
kaddari ku kayi auren ba wani mutuncin ki zai gani ba, zai
kuma rika zargin ki. Yana tunanin bada shi kadai kika saba ba.
Yar uwa ki kula, in wannan bai taba farowa da ke ba, na
tabbatar da ya faro da kawar ki ko yar uwar ki.


Daga karshe duk wanda ke da wasu alamu da za su tabbatar
mana cewa Namiji yana son mace banda wadannan, sai ya danna akwati mai
dauke da 'leave reply' yayi comment Ina maku fatan alkhairi da samun
abokanan rayuwa na kirki wanda za su so ku, so na gaskiya.

No comments:

Join our WhatsApp group

Join our WhatsApp group
Latsa nan domin shiga group din mu na whatsapp
Powered by Blogger.