ILLAR RASHIN YI WA JUNA KALAMAN SOYAYYA TSAKANIN MA'AURATA

KALAMAN SOYAYYA A TSAKANIN
MA'AURATA
.



Ma'aurata suna daukar duhun Kai ko in ce
girman Kai a kan nuna wa junansu
soyayya bayan AURE. Wanda yana Daga
cikin Babban gibin da auren yake samu.
Misali.

Ya kamata na miji ya dinga daurewa ko
kakane yana nunawa matar sa soyayya.
Yana gaya Mata maganganun soyayya
irin su.

1 INA SONKI
2 INA KAUNARKI
3 KE CE MACEN DA NAFI SO A DUNIYA
4 ko Kazan nan yayi miki kyau da dai
sauran maganganun na nuna soyayya da
kulawa.
Wanda haka zai sa taji itama ba ta da
masoyi daya fi shi. Kuma wannna
kalmomin ba zasu taba bacewa ba a
cikin kwakwalwarta.
.

Kuma zasu ta dinga yawan nishadi da jin
ita Mai sa'a ce a rayuwar aurenta.
AMMA DAN ALLAH KANA NUNA MATA
IRIN HAKA A RAYUWAR AURE KU ?
DAN UWA KA GYARA KADA KA BARI TA
DINGA JI A BAKI WASU HAKAN ZAI
BATA DAMAR TSANA A RAYUWAR AURe
KU.

 HAKA idan mace ce take gayawa mijinta
Yar uwa soyayya bata tsufa a wanna
rayuwa koda kina da shekara 80 kice
masa.
.
Yallabai Ina son ka.
Dear I love you.
Kai ne mijin da kafi kowanne birge Ni. ko
ta ce ai Ni duk wani Abu da kake so Ina
son shi.
ko in zai fita kice Allah ya dawo min da
Kai lafiya. ko in yayi kwalliya kice kayi
kyau fa darling. Da sauran maganganun
nuna soyayya da kambama shi kina nuna
yafi kowa. Wannan zai sa ki kara soyuwa
a zuciyarsa, ki zama ta gabab goshinsa,
kullum ya dinga jin sonki da son
kusantar ki, ya kuma tabbatar a ransa kin
Riga kin
sallama masa, sai shi ma ya sallama ki,
Amma sabanin hakan yawancin
ma'aurata sai
girman Kai.
kunya da Jan aji ya Hana su yin irin
wannan al'amarin da yake rage shakuwa
a tsakanin ma'aurata.

No comments:

Join our WhatsApp group

Join our WhatsApp group
Latsa nan domin shiga group din mu na whatsapp
Powered by Blogger.