WANE NE ABOKI NA GARI? DAGA BAKIN ANNABI DA SAHABBAI

ABOKI NA GARI 👉🏼Annabi SAW yana cewa:- "Mutum yana tafiya ne akan dabi'ar Abokin sa. Don haka kowa a cikinku ya duba yaga da wa ya kamata yayi abota". 👉🏼Sayyadina Uma.r Allah ya kara masa yarda yana cewa: "Babu wata ni'ima bayan ni'imar musulunci data wuce abaka aboki nagari. Don haka duk wanda ya dace da aboki nagari a cikin ku yayi riko dashi Qaaam". 👉🏼Imamul-shafi'I Allah ya jikan sa da rahama yana cewa:- "In Allah ya azurta ka da aboki nagari to ka rike shi Gam da hannunka, Domin samun Aboki nagari abune me wahalar gaske, kuma rasashi abu ne mai saukin gaske". 👉🏼Imam Hasanul Basari yana cewa:- "Muna son Abokan mu nagari fiye da yanda muke son Iyalanmu da 'ya'yan mu. Domin iyalan mu da 'ya'yan mu suna tuna mana Duniya. Shi kuma Aboki Nagari yana tuna mana Lahira ne, Yace yana daga Siffar Aboki nagari ya fifita bukatarka akan tasa bukatar". 👉🏼Luqmanul Hakim yake cewa da 'Dansa.Ya kai 'Dana, farkon Abunda zaka tsururuta arayuwar ka bayan imani da Allah shi ne Aboki nagari. Domin Aboki na gari tamkar bishiya ce, in ka zauna akasanta, sai inuwarta ta lullubeka gabarin Rana. In ka tsinki Dan itacenta ta kosar dakai daga yunwa. In har bata anfanar da kai ba kuma bazata taba cutar da kai ba. Allah ka bani Aboki nagari, kasa in zama nagari da kuma sauran al'ummar musulmai bakidaya. 👉🏼duk aboki nagari zai so wannan sako zuwa ga abokinsa, don ya samu falalar abin da zai zama alkhairi agareshi. da sauran Musulmi... GODIYA GA ABOKAINA NAGARI!!!

No comments:

Join our WhatsApp group

Join our WhatsApp group
Latsa nan domin shiga group din mu na whatsapp
Powered by Blogger.