TAKAICI: WATA TSALELIYAR BUDURWA TA AURI KARE A KASAR INDIYA


Wata tsaleliyar budurwa ta auri kare a kasar Indiya - Budurwar mai shekara 18 a duniya mai suna Mangli Munda ta auri angonta karen mai suna Sheru - Dangin amaryar dai sun yadda cewa idan har ta fara auren mutum to masifa da bala'i za su kewaye dangin su, hakan ne ya sanya dole sai ta fara auren kare sannan daga baya ta auri mutum 

Budurwar mai shekara 18 a duniya mai suna Mangli Munda ta auri angonta karen mai suna Sheru - Dangin amaryar dai sun yadda cewa idan har ta fara auren mutum to masifa da bala'i za su kewaye dangin su, hakan ne ya sanya dole sai ta fara auren kare sannan daga baya ta auri mutum

 Wata budurwa 'yar shekara 18 a duniya dake kasar Indiya ta auri kare, an yi bikin wannan aure ne a gabashin jihar Jharkhand dake kasar ta Indiya. Komai dai ya tafi yadda ya kamata, domin kuwa an yiwa amarya ado, an gayyato 'yan uwa da abokanan arziki, an rabawa sama da mutane saba'in abinci, sannan kuma an shirya wajen bikin kamar dai yadda aka saba.

 Budurwar 'yar shekara 18 mai suna Mangli Munda ta auri mijinta kare mai suna Sheru. Manya a cikin danginta sun bayyana cewa idan har ta auri mutum namiji to tabbas za ta kawo musu bala'i cikin dangi, hakan ya sanya ta aurar karen.

No comments:

Join our WhatsApp group

Join our WhatsApp group
Latsa nan domin shiga group din mu na whatsapp
Powered by Blogger.