Rikici: Wani saurayi ya kashe mahaifinsa har lahira ta hanyar caka mishi kwalba bayan yasha kwaya ya bugu ya yi mankas

Wani saurayi da ya kashe mahaifinsa har lahira ya bayyana cewa ya sha kwaya ne ya bugu yaje ya kashe shi An bayyana cewa rikici ne ya kaure tsakanin saurayin da mahaifinsa kawai sai ya fara dukan shi har yayi amfani da wata kwalba ya caka masa, shi kuwa ya ce ga garinku nan Dama dai an ce ba wannan ne karo na farko da suka fara wannan rikici ba, sun saba yin irin hakan 


Wani saurayi dan shekara 20 a duniya ya shiga hannun jami'an 'yan sanda bayan an kama shi da laifin dukan mahaifinsa mai shekaru 65 har yayi sanadiyyar mutuwarsa. 

Wannan lamari dai ya faru ne a kauyen Umuaro dake cikin karamar hukumar Ehime Mbano dake cikin jihar Imo. 

KARANTA KUMA: Wata kyakkyawar budurwa ta mutu bayan babbar aminiyarta ta saka mata guba a abinci saboda ta samu karin girma a wajen aiki

Matashin saurayin wanda aka bayyana sunansa da Ikechukwu Munahawu, ya kashe mahaifinsa mai suna Mr. Patrick Munahawu da wata fasasshiyar kwalba, sai dai kuma ya bayyana cewa yayi wannan aika-aika ne saboda kwayar da ya sha. 

Wani jami'in dan sanda da yake aiki a ofishin 'yan sanda dake Ehime Mbano, ya nemi a boye sunansa, ya ce marigayin ya mutu ne bayan wani rikici da suka yi da babban dan nasa. 

Haka kuma wasu rahotannin sun bayyana cewa 'yan uwan marigayin sun bayyana cewa matashin saurayin ya sha yin rikici da mahaifin nasu ya dinga marin shi akan idon kannanshi. 

No comments:

Join our WhatsApp group

Join our WhatsApp group
Latsa nan domin shiga group din mu na whatsapp
Powered by Blogger.